Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gwamnatin Amurka a ranar Juma'a ta sanar da cewa za ta sanya wa kamfanin sinadarai na "Hengli" dake birnin Dalian mai tashar jiragen ruwa a arewa maso gabashin China takunkumi saboda siyan man fetur daga Iran.
Gwamnatin China, wacce gaba daya ita ce babbar abokiyar cinikin man Iran, a yau ta nuna rashin amincewarta ga wannan yunkurin na Amurka. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China ya ce: "Mu a kodayaushe muna adawa da takunkumin bangare daya da aka kakaba wa wata kasa ba bisa doka ba da rashin tushe. Amurka ta daina yin kurakuran ta na yin amfani da takunkumi da aiwatar da ikon da ya wuce iyakokinta".
Your Comment